Rahotanni sun ce a ƙalla mutum 150 ne suka mutu cikin kwana biyu a rikice-rikice tsakanin Hausa da wasu ƙabilun jihar Blue Nile da ke Sudan.
Rikicin shi ne mafi muni a cikin watannin baya-bayan nan.
Faɗan ya ɓarke ne a makon da ya wuce kan rikicin fili tsakanin Hausawa da ƙabilun da ba sa ga maciji, inda aka kashe fiye da mutum 12 suka mutu.
Tuni aka saka dokar hana fita don shawo kan rikicin.
BBC ta rawaitu cewa majalisar Dinkin Duniya a ranar Alhamis ta ce “akwai fargabar rikicin ya ƙara muni a Lagawa da kuma yankin jihar Blue Nile.
“Ba za a taɓa samun zaman lafiya mai ɗorewa ba idan har babu sahihiyar gwamnati da za ta fifita buƙatun al’ummominta da suka haɗa da tsaro da magance abin da ke jawo rikici,” a cewar Ofishin MDD da ke taimaka wa wajen mayar da ƙsar tsarin dimokraɗiyya, a wata sanarwa.
Sudan ta jima tana fama da rikicin siyasa da tashe-tashen hankula tun bayan juyin mulkin da aka yi a ƙasar a bara.











































