Abba Kyari: Yadda na Biya Cin Hanci Wajen Shigo da Hodar Iblis- Shaida a Kotu 

NDLEA and Abba Kyari
NDLEA and Abba Kyari

Wani da aka kama da laifin safarar hodar iblis, Emeka Ezenwanne ya bada shaida a kotun tarayya dake garin Abuja a shari’ar NDLEA da Abba Kyari.

Premium Times tace Ezenwanne ne shaida na biyar da hukumar NDLEA ta gabatar, ya kuma yi bayanin yadda ya bada cin hanci wajen shigo da kwayoyi. Kamar yadda Ezenwanne ya fadawa kotu da bakinsa, ya ba jami’an tsaron da ke aiki a filin jirgin Akanu Ibiam N10, 000, domin ya wuce dauke da hodar iblis.

Wannan mutum wanda yanzu yana daure a gidan yari da ke garin Suleja, yace an dauko hodar iblis din ne daga kasar Brazil, aka biyo da shi ta Habasha. Mai bada shaidar ya fadawa Lauyan NDLEA, Joseph Sunday cewa ya je birnin Addis Ababa a tsakiyar Junairu domin ya karbo kwayoyi daga kasar Brazil.

“A ranar 16 ga watan Junairu da kimanin karfe 8:30 a agogon kasar Habasha, jirgin da ya zo daga Brazil ya sauka. Jim kadan bayan nan aka kira ni a waya, Mutumin farko da ya kira ni a wayar salula, ana kiransa Alhaji  Emeka Ezenwanne.”

“A ranar 19 ga watan Junairu da kimanin karfe 8:00 na safiya, muka hau jirgin da zai sauka filin sauka da tashin jiragen sama da ke garin Enugu. Da muka isa filin jirgi, na fito na zauna a mota, ina jiran wanda muke tare da shi (Umeibe), ya fito.”

“Daga nan aka fara samun matsala, ‘yan sanda a cikin fararen kaya da muka gane cewa dakarun IRT ne, suka tare kayan da Umeibe ya dauko. A filin jirgin saman Enugu, an bukaci In biya kudi ga mutanen da za su duba jaka ta. Saboda haka sai na biya su N10, 000, suka kyale ni na wuce.”

Ezenwanne yana cewa daga baya ‘yan sandan suka fito da rigunansu, sai ya fahimci ‘yan IRT ne, a karshe suka cinna shi ga NDLEA. Da aka zo gaban jami’an NDLEA, Ezenwanne yace adadin kwayoyin da suka shigo da su ya ragu, amma yace duk abin da aka yi, bai hau da DCP Abba Kyari ba.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here