Jam’iyyar (PDP) ta sanar da dakatar da sakatarenta na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, tare da Mashawarcinta Kamaldeen Ajibade, da wani jami’i saboda zargin karya dokokin jam’iyya.
Hukumar gudanarwa ta ƙasa ta jam’iyyar (NWC) ce ta dauki wannan mataki bayan wani zama da ta gudanar a Abuja a ranar Asabar.
Jam’iyyar ta bayyana cewa an dakatar da jami’an na tsawon wata guda yayin da kwamitin ladabtarwa zai gudanar da bincike kan laifukan da ake tuhumar su da aikatawa.
A cewar jam’iyyar, mataimakin sakataren ƙasa, Hon. Setonji Koshoedo, zai rike mukamin sakataren ƙasa na wucin gadi a wannan lokaci.
Har ila yau, an umurci daraktan sashen shari’a na jam’iyyar da ya kula da ayyukan ofishin Mashawarcinta da mataimakinsa har sai an kammala bincike.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wata kotun tarayya a Abuja ta hana gudanar da babban taron jam’iyyar da aka shirya saboda zargin rashin bin ka’idojin jam’iyya wajen shirye-shiryen taron.
Rahotanni sun nuna cewa akwai rikici mai tsanani tsakanin sakataren ƙasa da shugaban riko na jam’iyyar, Umar Damagum, wanda ya jawo wannan matakin na dakatarwa.













































