Wani fursuna da aka yanke wa hukuncin kisa mai suna Abba Hassan ya tsere daga gidan gyaran hali da ke Potiskum, a jihar Yobe, da safiyar ranar Juma’a, 31 ga Oktoba, 2025.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar Yobe, SP Dungus Abdulkarim, ya bayyana cewa wanda ya tsere ɗan asalin Maiduguri ne a jihar Borno.
A cikin sanarwar, rundunar ta shawarci jama’a, jami’an tsaro, shugabannin al’umma, masu jigilar fasinjoji da ƙungiyoyin sa-kai a cikin jihar da makwabtanta su kasance cikin shiri, su kuma bayar da rahoto idan sun ga ko sun samu wani bayani da zai taimaka wajen kamo fursunan.
An kuma gargadi jama’a da kada su kuskura su yi ƙoƙarin cafke shi da kansu, sai dai su sanar da ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko kuma hukumar gyaran hali mafi kusa, ko su kira lambar gaggawa 08038452982.
Rundunar ta kuma roƙi jama’a da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro haɗin kai domin tabbatar da tsaron jama’a da kuma sake kama wanda ya tsere daga gidan gyaran halin.













































