Gwamnatin Katsina ta hada kwamatin da zai binkice dalilin kisan basaraken da yan bindiga sukai

Dr. Dikko Umar Radda 750x430
Dr. Dikko Umar Radda 750x430

Gwamnatin jihar Katsina ta hada kwamitin da zai binkice dalilin kisan dakacin kauyen Dabaibayawa dake karamar hukumar Batagarawa a jihar.

Isah Miqdad, wanda shine mai taimakawa gwamnan jihar kan harkokin yada labarai ne ya bayyana hakan ranar  Litinin a Katsina, inda yace kisan ya faru ne mako biyu da suka wuce.

“Domin gano dalilin garkuwa tare da kisan dakacin kauyen Dabaibayawa, gwamnatin jihar Katsina ta hada kwamitin da zai yi binkice akan faruwar lamarin.”

“Wanda kuma mataimakin gwamna, Malam Faruk Lawal-Jobe ne zai jagoranci kwamitin,” Inji Miqdad.

Ya kuma kara da cewa kwamitin nada sati biyu domin kawo wa gwamnati rahoton sa.

Masarautar Katsina ta yabawa gwamnan tare da gode masa bisa kokarin sa na ganin an kama wadanda suka aikata wannan danyan aikin, sanan kuma masarautar ta bada tabbacin bada duk wata gudun mawa idon bukatar hakan ta tashe.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here