Gwamnatin Kano ta kalubalanci tsarin raba kayan rage radadi na biliyan 500 da gwamnatin tarayya ke shirin yi

Kano NNPP Governorship Candidate Abba Kabir Yusuf.
Kano NNPP Governorship Candidate Abba Kabir Yusuf.

Gwamnatin jihar Kano ta kalubalanci tsarin gwamnatin tarayya na raba biliyan 500 ga kananan kamfanonin kasar nan domin rage radadin ciretallafin man fetur.

Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf, ya kalubalanci tsarin ne a gurin wani taro da ya yi da kungiyar Kano Cooperative Society a gidan gwamnatin jihar ranar Alhamis.

Ya ce akwai rashin adalci a cikin tsarin rabon, inda ya kara da cewa  jihar Legas ita kadai ta ja kaso 47, sai kuma jihohin kudu masu kudu da suka ja kaso 17, ya yin da ragowar shiyoyin kasar aka basu rabon da bai taka kara ya karya ba.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin mataimakin sa, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya sake jaddada anyar gwamnatin sa wajan kawar da fatara da talauci a jihar ta Kano.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun mataimakin gwamnan, Ibrahim Shuaibu ya fitar a ranar Juma’a.

A cikin sanarwar gwamnan ya bayyana tsarin a matsayin rashin adalci kuma ya sabawa tsarin kundin mulkin kasar nan, sanan kuma ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da majalisar wakilai da su dau mataki akan wannan lamari.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here