Babban layin lantarki na ƙasa ya samu wata matsala, lamarin da ya haifar da ɗaukewa lantarkin a wasu sassan ƙasar nan, tare da jita miliyoyin mutane cikin duhu..
Cikin wata sanarwa da kamfanin rarraba wutar lantarki na birnin Abuja ya fitar a shafinsa na X, ya ce matsalar ta faru ne da misalin ƙarfe 11:34 na safe.
Sai dai kamfanin ya ce masu ruwa da tsaki na aiki tuƙuru domin maido da wutar da zarar an magance matsalar.
Karin karatu: Yawan ƙarin kudin lantarki na barazana ga masana’antu – MAN
Babban layin lantarki na Najeriyar ya saba samun matsalolin faɗuwa, musamman a shekarar da ta gabata, wani abu da ke haifar da matsalar ɗaukewar wutar a faɗin ƙasar nan.
Wannan dai shi ne karo na farko a shekarar 2025 da babban layin lantarkin ya samu matsala, bayan sa shekarar 2024 matsalar ta ta’azzara,