Gwamnatin ƙasar Amurka ta sanar da cewa za ta dakatar da bayar da biza ga ‘yan Najeriya da kuma ‘yan ƙasashe 18 daga ranar 1 ga watan Janairu, 2026.
Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce matakin ya biyo bayan wata dokar shugaban ƙasa mai lamba 10998 da ta shafi tsaron ƙasar.
Sanarwar ta bayyana cewa dakatarwar za ta shafi biza na yawon buɗe ido na B-1 da B-2, da biza na ɗalibai da musayar karatu na F, M da J, da kuma yawancin biza na zama na dindindin.
Sai dai an ware wasu rukuni na musamman da suka haɗa da ‘yan ƙabila ko addinai da ake tsananta wa a Iran, masu ƙasashe biyu da ke amfani da fasfo na ƙasar da ba a sanya wa takunkumi ba, da kuma wasu keɓaɓɓun shari’o’i.
Ofishin jakadancin ya ce dokar shugaban ƙasa mai lamba 10998 za ta fara aiki ne daga ƙarfe 12:01 na dare agogon gabashin Amurka a ranar 1 ga watan Janairu, 2026.
Hakan na nufin za ta shafi mutanen da ke wajen Amurka a wannan lokaci kuma ba su da biza mai inganci a hannunsu a ranar da dokar ta fara aiki.
Sanarwar ta kuma jaddada cewa duk wanda ke da biza mai inganci kafin ranar fara aiwatar da dokar ba zai fuskanci soke bizar ba.
Haka kuma, an tabbatar da cewa babu wata biza da aka bayar kafin wannan ranar da aka soke ko za a soke sakamakon wannan doka.
Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya ƙara da cewa masu neman biza da wannan doka ta shafa za su iya ci gaba da cike takardun neman biza da kuma ɗaukar alƙawarin tattaunawa, amma hakan ba lallai ba ne ya kai ga bayar da biza ko shigar su ƙasar Amurka.
Dokar, wadda aka fitar a ranar 16 ga watan Disamba, 2025, na da nufin takaita shigowar ‘yan ƙasashen da ake kallon suna da barazana ga tsaron Amurka, ciki har da Najeriya.
A halin yanzu, wasu ‘yan Najeriya sun fara bayyana rashin jin daɗi kan wannan mataki, musamman dangane da asarar kuɗin da suka kashe wajen neman biza da kuma tasirin da hakan zai iya yi a rayuwarsu.
Wannan mataki ya haifar da muhawara mai zafi a kafafen sada zumunta, inda wasu ke nuna damuwa kan tasirin tattalin arziki da na tunani da dakatarwar za ta haifar ga masu neman biza.













































