Gwamnatin Katsina Ta Kori Basarake Bisa Gudanar Da Daurin Aure Ba Bisa Ka’ida Ba

0
Dikko Umar Radda 750x430

Gwamnatin jihar Katsina ta kori Hakimin Kuraye, Alhaji Abubakar Abdullahi-Ahmadu.

A wata sanarwa da Daraktan hulda da manema labarai, Alhaji Abdullahi Aliyu-Yar’adua ya fitar, ta ce matakin ya biyo bayan shawarar da masarautar Katsina ta bayar.

“An kama Abdullahi-Ahmadu da lefin gudanar  da daurin aure ba tare da an gabatar  masa da takardar shaidar likita ba kamar yadda doka ta tanada.”

“Sakamakon dauren da yayi, an gano daya daga cikin ma aure tan yana da cutar kanjamau; Hakimin ya jagoranci daurin auren ba tare da bin ka’ida ba,” in ji sanarwar. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here