Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta kama wani matashi dan shekara 36, Ja’afar Adamu, bisa zargin yi wa matar makwabcin sa ‘yar shekara 21 fyade uguwar Diocese da ke karamar hukumar Hong.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar PPRO, SP Suleiman Nguroje ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Yola ranar Talata. Nguroje ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar 15 ga watan Satumba.
Jami’in ya bayyana cewa ana zargin mutumin da shiga gidan makoci sa bayan ya fahimci ya tafi gona, inda ya rufe fuskar don kada a gane shi.
Ya kara da cewa “wanda ake zargin ya zarewa matar wuka domin ya tsorata ta bashi hadin kai, inda garen biyawa kansa bukata kallen da ya rufe fuskar sa dashi ya yaye daga fuskar sa, ita kuma ta gane shi.”