Bayanin hakan na dauke a wata takarda wacce jami’in hulda da jamaa na kungiyar Mukhtar Gwammaja ya sanyawa hannu aka rabawa manema labarai a kano.
Ta cikin takardar Jagoran kungiyar Barrister Abdulziz yace manufar Kungiyarsu shi ne tabbatar da ci gaban siyasa ga al’ummar Jihar Kano dama kasa baki daya.
“Tare da sallama irin ta addinin musulunci, da fatan alkhairi ga alumar jihar Kano musamman magoya bayan jamiyyar APC Muna Mai gabatar da wannan sabuwar tafiya Mai suna We#standwith Danzago Dan ci gaban jamiyyar APC a jihar kano da kasa baki daya.”
“Wannan kungiya na Kuma Kara jaddada goyon bayan ta ga Mai girma Ambassador Amadu Haruna Zago.” Inji shi.
Kazalika Abdul’aziz, ya Kuma yi Kira ga daukacin yayan jamiyyar APC da su Yi hakuri su zauna a jamiyyar APC Dan ci gaban kasa.
Yace tallata manufofin jamiyyar APC a jihar kano Don samun nasara a manyan zabubbukan shekara mai zuwa ta 2023 tare da kare martaba da mutuncin Mai girma Ambassador Amadu Haruna Zago, wasu daga cikin manufofin Kungiyar.
Ya kara da cewa tuntuba da ziyarar Yan jamiyyar APC a kanaanan hakumomi 44 Don wayar da al’umma kan a zabi jamiyyar APC a jihar kano da kuma gabatar da tarruruka a unguwanni Don samun nasarar jamiyyar APC a jihar Kano, suma na cikin manufofin tafiyar.
Kungiyar dai tana tafiya ne karkashin shugabancin, Barrister Abdulaziz, a matsayin Shugaba, sai Hajiya Amina kamilu matsayin mataimakiyar shugaban da kuma Dakta Abdulkadir Ahmad Jogana dake a matsayin Sakatare.
Yayin da Mohd Yakubu Dan-Hassan ke matsayin mataimakin Sakatare, Hussain Dan Mukulli a matsayin Sakataren Tsare-tsare, sai kuma Mukhtar B.A.A Gwammaja Jami’in yada labarai, Muhammad Uba Sukilala ke matsayin Ma’aji.
Sauran sune Hajiya Aisha Ibrahim Shugabar Mata, da Dakta Suleiman Isyaku shugaban matasa, da Barrister Rabiu Saidu mai bada shawara kan harkokin shari’a da kuma Miftahu Ishaq mai binciken kudi.












































