Yajin Aiki: Kungiyar ASUU ta zauna domin yanke hukunci na gaba

ASUU ASUU NEW 660x381 1
ASUU ASUU NEW 660x381 1

Majalisar Zartarwar kungiyar malaman Jami’o’i ta kasa ASUU ta dugunar da wani taro a daren ranar Lahadi a Abuja domin tattaunawa kan yajin aikin kungiyar na tsawon makwanni 12.

An yi tunanin a taron kungiyar zata yanke hukuncin ci gaba da yajin aikin ko kuma dakatar da shi.

Tun a ranar 14 ga watan Fabrairun shekarar 2022 ne dai kungiyar ta ASUU ta tsunduma yajin aikin gargadi domin Gwamnatin Tarayya ta biya musu bukatunsu.

Bukatun sun hadar da Gwamnatin ta cika alkawarin yarjejeniyar da suka kulla a watan Disambar shekarar 2020, kan samar da kudaden da za a farfado da Jami’o’in Gwamnati.

Sauran bukatun sun hadar da biyan alawus-alawus da sauran hakkoki na Malaman jami’a da Gwamnatin ta yi musu alkawari tun a shekarar 2009 da sauransu.

Haka kuma Kwamitin shugabannin Jami’o’i ta Najeriya sun jaddada bukatar dake akwai ta ganin an samu daidaito tsakanin kungiyar ASUU da Gwamnatin Tarayya.

Shugaban Kwamitin Farfesa Samuel Edoumiekumo, ne ya bayyana hakan a zantawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasar NAN ranar Lahadi a Abuja babban Birnin Najeriya.

Yace yana da matukar muhimnanci ga duka bangarorin biyu a cimma matsaya domin kawo karshen yajin aikin da ya ki ci yaki cinyewa.

Ya kuma bukaci duka bangarorin biyu dasu martaba yarjejeniyar da aka kulla tsakani don gudun kawo tazgaro ga harkokin karatun Jami’o’i a Kasar.

A ranar Juma’a ne dai Ministan Kwadago da samar da ayyukan yi na Kasar Sanata Chris Ngige, ya bayyana cewa Gwamnatin tarayya da kungiyar ta ASUU zasu koma teburin tattaunawa domin samun maslaha a wannan Makon.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here