Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da harin da aka kai a wasu yankuna na jihar Zamfara a baya-bayan nan.
Idan za a iya tanawa dai a kalla mutune 55 ne suka rasa rayukansu a mabambantan hare-haren da aka kai garuruwa 4 na jihar ta Zamfara a cikin kwanaki 3.
Garuruwan da aka kai harin sun hadar da Sabon Gari Damri da Damri, da kuma Kalahe a yankin karamarHukumar Bakura, sai kuma Faru a yankin Karamar hukumar Maradun duka dai a jihar ta Zamfara.
A cikin wata sanarwa da babban mai taimakawa shugaban Kasa kan harkokin yada labarai Garba Shehu, ya fitar a ranar Lahadi, shugaba Buharin ya bukaci Dakarun Sojin Najeriya da su yi duk mai yiwa wajen ganin sun dakatar da kashe-kashen da ‘Yan ta’addar ke yi a Kasar.
Ya kuma nuna alhini tare da mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalai, ‘Yan uwa, Gwamnati da kuma al’ummar Jihar, bisa Kisan ta’addanci da aka yiwa Yan uwansu.
Shugaban Kasar ya kuma yaba da irin kwazon da Dakarun Sojin Najeriyar ke yi wajen ganin sun kawo karshen matsalar rashin tsaro, musamman a yankunan Arewa maso Gabas da kuma Arewa maso yamma.













































