Masana’antar Dangote ta ƙawata bikin baje kolin kayayyaki a birnin Lagos

Dangote stand at trade fair 1
Dangote stand at trade fair 1

Katafariyar masana’antar Dangote da ta shahara a nahiyar Afrika na cigaba da ƙawata bikin baje kolin nuna kayayyaki da ke gudana a birnin Ikko, da nau’ikan kayayyaki 5 da kamfanin ke sarrafawa.

Jaridar solacebase ta ruwaito cewa manyan kayan kamfanonin dangote dake baje kolin sun haɗa da kamfanin Nascon da ke sarrafa Gishiri da rukunin kamfanonin samar da Sikari Taki da kuma kamfanin matatar man Fetur duk mallakin Dangote.

Sanarwar ta ce, bikin baje kolin wani bangarene na gabatar da sabbin kayayyaki ga al’umma domin sayen kayayyaki cikin farashi mai sauƙi.

“Kun ga tuni aka fara yin takin Dangote kuma zamu bada dama ga dimbin kwastomomi da manoma waɗanda ke neman ƙarin haske game da yadda ake amfani da wannan taki”.

“Kuma mun samar da kwararru da za su amsa tambayoyin mutane game da yadda ake amfani da takin da sauran kayayyakin mu la’akari da ƙaratowar karshen shekara”.

Sanarwar ta ce, kamfanin NASCON da ke samar da Gishiri da kayayyakin ɗanɗanon girki zai raba kayayyaki masu nauyin giram 250 da giram 500 da kuma masu nauyin kilogram 1, yayin da masana’antar ta ce, matatar man Fetur ta Dangote zata yi baje kolin irin kayayyakin da take sarrafawa don nuna su ga dimbin jama’a da suka halarci taron.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here