Kasar Birtaniya ta ayyana karin kudi sama da fam miliyan 95 dan kulada sha’anin aikin noma da sauyin yanayi a Najeriya.
Sakataren harkokin wajen Birtaniya James Cleverly ne ya sanar da wannan alkawarin a taro karo na 27 kan sauyin yanayi da ke gudana a birnin Sharm El Sheikh na kasar Masar.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya rawaito cewa shirin Propcom+, shiri ne na Asusun Kula da yanayi na burtaniya wanda ke da nufin tallafawa sauyin tattalin arziki a sasannin Najeriya.
Rahotanni sun ce alwashin da birtaniyar tayiwa Najeriya ya kunshi wani bangare na tallafin da Burtaniya za ta bayar na sama da fam miliyan 100 ga kasashe masu tasowa don tunkarar sauyin yanayi.
Cikakkun bayanan tallafin ya nuna cewa akalla ‘yan Najeriya miliyan 4 da suka hada da mata miliyan 2 ne za su amfana, domin samar da kayayyakin dasuka dace dan tunkarar illolin sauyin yanayi.
“Shirin ze yi aiki tare da kamfanoni masu zaman kansu a Najeriya kan harkar noma don kara samar da albarkatun kasa, inganta abinci mai gina jiki da samar da abinci, rage fitar da hayaki.
A jawabin sa, Cleverly ya ce: “Yarjejeniyar sauyin yanayi ta Glasgow ta baiwa duniya tsari na musamman domin iyakance hauhawar dumamar zafin duniya zuwa digiri 1.5.
Da yake tabbatar da tallafin, mataimakin babban kwamishinan Burtaniya a Najeriya Ben Llewellyn-Jones, ya ce Najeriya na da matukar cikin barazana kan sauyin yanayi.










































