‘Yan sanda sun cafke Dan Jam’iyyar APC da katunan zabe a kano

KATINEN ZABE
KATINEN ZABE

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama wani mutum mai suna Tasiu Abdullahi Hayin Hago bayan da aka samu rahoton cewa an same shi da katunan zabe 29 na wasu mutanen da ba su ji ba gani ba, wanda ya saba wa dokar zabe ta 2022 da aka yi wa kwaskwarima.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Abdullahi Kiyawa ya shaida wa Solaceba cewa, wanda ake zargin mai shekaru 45, an kama shi ne a Dawaki dake karamar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano.

Kiyawa ya ce bisa ga bayanai da sa ido, an ga wanda ake zargin dauke da kwafi 29 na katin zabe na dindindin (PVCs) a wata cibiyar kasuwanci da ke daukar hotunan katunan da ake zargin.

Sai dai ya ce an mika wanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka na rundunar ‘yan sandan jihar Kano domin gudanar da bincike mai zurfi.

Yayin da yake amsa tambayoyi bayan kama shi a sashin binciken manyan laifuka na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, an tattaro cewa wanda ake zargin yace dan gwamnan jihar Kano Abba Ganduje ne kuma dan takarar jam’iyyar APC na Dawakin Tofa, Rimingado da kuma Rimingado ne ya sanya shi.

“Dan takarar mu Abba yana son katin zabe na N10,000 ga mutanen da suka yarda su zabe shi, ku ba ni PVC don ci gaba da aiki na” wanda ake zargin ya sake nanata hakan a wani bangare na martanin da aka rubuta a cikin fayil din karar.

Sai dai ko da Solacebase da ta tuntubi dan takarar jam’iyyar APC mai wakiltar mazabar Dawakin Tofa da Rimingado da Tofa na tarayya, Abba Ganduje kan batun amma layukan wayar sa arufe.

Shugaban jam’iyyar na jihar, Alhaji Abdullahi Abbas ya shaida wa Solacebase cewa bai da masaniya amma ya yi alkawarin gudanar da bincike tare da maida jawabi ga wannan jarida.

‘’Gaskiya ban san an kama wani dan jam’iyyar mu da ‘yan sanda suka yi ba. Ka ga abin da mutane suka kasa gane a wannan rana INEC ta ce babu wani mutum daya da zai iya yin amfani da PVC na wani,’’ inji Abdullahi Abbas.

A halin da ake ciki, a wata sanarwa da Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, babban mai magana da yawun NNPP na yakin neman zaben 2023 ya ce jam’iyyar ta umurci tawagar lauyoyin ta karkashin mashawarcin kan shari’a na jihar Barr. Bashir Yusuf Tudun wuzirchi ya ci gaba da bin diddigin lamarin tare da tabbatar da gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotun da ke da hurumin hukumta don fuskantar fushin doka.

“Idan za ku iya tunawa a kwanakin baya ne aka yanke hukunci kan irin wannan shari’a da ake yi wa shugaban jam’iyyar APC na Yautar Arewa a karamar hukumar Gabasawa ta jihar Kano,” in ji Bature.

Sunusi Bature ya kara jaddada bukatar ‘yan uwa dasu kai korafi tareda kai rahoton abubuwan da suka faru a irin wannan yanayi Dan kare tsarin dimokuradiyya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here