Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya amince da dakatar da Alhaji Mohammed Wada-Yahaya, Manajan Daraktan Hukumar Raya Birane ta Jihar Nasarawa bisa zargin lalata allunan yakin neman zabe.
Dakatarwar na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Sakataren Gwamnatin jihar Malam Muhammed Ubandoma a Lafia.
Sanarwar ta kara da cewa MD na kan dakatarwa ba tare da biyan albashi ba har sai an kammala bincike kan lamarin.
“Akwai jerin korafe-korafe game da lalata allunan talla da ‘yan siyasa da magoya bayansu suka kafa ba gaira ba dalili; da nufin yin katsalandan a zaben 2023, ciki har da jam’iyya mai mulki.
“Lalata allunan talla ba tare da wani dalili ba, daidai yake da rashin biyayya da rashin da’a,” in ji gwamnati.













































