Gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi sun raba kuɗin shiga da ya tasamma Naira miliyan dubu 740 cikin kuɗaɗen shiga da gwamnatin tarayya ta samu a watan Satumban da ya gabata.
Hakan na ƙunshe ne cikin takardar bayan taro da aka raba wa manema labarai yayin taron ƙarshe da kwamitin raba tattalin arziki ya gudanar na wannan watan da muke ciki na Oktoba.
Sanarwar ta ce, cikin wannan adadi na kuɗi da ya ƙunshi Naira milyan dubu 577 daga kudaden haraji dakuma wasu karin kudi kimanin Naira Milyan Dubu 3 daga rarar kudade asusun tarayya.
“A watan satumba 2021 min Sami kimanin naira Milyan Dubu 126 daga kudaden ajiya da na rarar aikace aikace”
” Saboda haka muna da jumullar dala miliyan 61 daga kudaden rarar hada hadar albarkatun man fetir”
Sanarwar ta tabbatar da cewa daga wannan adadi, gwamnatin tarayya ta sami naira Milyan Dubu 276, Inda matakan jihohi suka sami naira Milyan Dubu 140 yayin da kananan hukumomi suka sami naira miliyan dubu 107 bayanan cire kaso 13 dan baiwa jihohin da ake hako albarkatun man fetir.
“A watan satumba 2021 an sami kuɗaɗen shiga kimanin naira miliyan dubu 170 wanda ya gaza na watan Agusta da aka sami naira miliyan dubu 178.”
Sanarwar ta ce gudanar da taron, na da alaka da yadda za a lalubo hanyoyin dakatar da zirarewar kuɗaɗen haraji ga albashin ma’aikata.












































