Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje yace gwamnatinsa ta kammala dukkan shirin dasuka dace domin aikin hadin gwiwa da masu zuba hannun jarin kasar Denmark abangaren sarrafa shara.
Gwamnan ya bayyana hakane lokacin da yake karbar bakuncin jakadan kasar Denmark a Najeriya Mista Per Christensen Wanda ya kai masa ziyarar ban girma a gidan gwamnatin.
Awata sanarwar me dauke da sa hannun kakakin maaikatar Muhalli Sunusi kafar na’isa wadda aka rabawa manema labarai a Kano.
Jaridar solacebase ta rawaito cewa gwamna Ganduje yace jihar kano neman masu zuba hannun jarin dazasu dauki gabaren Shirin, domin lalubo hanyoyin sarrafa shara da sauran lalatattun kayayyaki izuwa abubuwa masu amfani.
Sanarwar tace Gwamna Ganduje ya kara dacewa kamata yayi hukumar tsaftar Muhalli ta sauya akalar yadda take gudanar da ayyukan ta ta yadda za ta rika samarda takin zamani da makamashin wutar lantarki daga sharar datake kwashewa.
” Babu shakka jihar Kano jiha ce mafi dimbin jamaa afadin najeriya, kuma shine birni na 2 Madi girma akasar nan, to ka ga kuwa duk Inda akace akwai dimbin jamaa, abi na farko da mutum zefara tunanin tunkara shine batun yadda za a sarrafa sharar da ake tarawa”.
” Hakane ya sa tunda jimawa muka cimma matsaya da kamfanin sarrafa shara na Cape Gate kasancewar abin da muke bukata yafi batutuwan damuka cimma matsaya kwarai da haske”. Daganan Ganduje ya godewa jakadan na kasar Denmark bisa wannan ziyarar, yana maicewa suna fatan wannan hadin gwiwa zai amfani kowanne bangaren ta hanyar inganta tattalin arzikin.
Dayake maida jawabi, Jakadan Christensen yace yazo Kano me domin tattauna yadda za a cimma matsaya tsakanin kasar sa da jihar Kano ta hannun kamfanin sarrafa shara na Cape Gate.
A tsokacin da yayi kwamishinoni Muhalli Alhaji Kabir Ibrahim getso yace jakadan ya ziyarci Kano me domin nazari tareda duba kan irin kayan aiki da kamfanin sarrafa sharar ke dashi musamman ayankunan ZAURA da wasu manyan cibiyoyin sarrafa shara dake fadin Kano.












































