Bashin Da Ake Bin Najeriya Yanzu Ya Doshi Tiriliyan 50 – DMO

0
Tinubu 8

Ofishin Kula da Basussuka na Kasa (DMO) ya ce jimillar bashin da ake bin Najeriya a yanzu ya kai Dalar Amurka biliyan 103.3, kwatankwacin Naira tiriliyan 49.8 ya zuwa ranar 21 ga watan Maris.

DMO ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.

Ofishin ya ce bashin ya kuma hada da kudaden da ake bin Jihohi da Gwamnatin Tarayya, sai dai ban da wanda Babban Bankin Najeriya (CBN) ke bin gwamnatin.

Sanarwar ta ce, “Ya zuwa karshen watan Maris din 2023, jimillar basussukan da ake bin Najeriya, wanda ya hada da na gida da na ketare da kuma na Gwamnatin Tarayya da Jihohi 36 da Abuja, ya kai Naira tiriliyan 49.8 (wato Dalar Amurka biliyan 108.30).”

“Amma adadin bai kunshi Naira tirliyan 22.7 din da CBN ke bin Gwamnatin Tarayya ba, wanda Majalisar Dokoki ta Kasa ta sahale wa gwamntin ciyowa a watan Mayun 2023. Shi wancan adadin za a saka shi a jerin basussuka na cikin gida daga watan Yunin 2023.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here