Mukaddashi Kayode Egbetokun, ya kafa kwamitin bincike mai mutum bakwai domin gudanar da bincike kan mutuwar wani matashi mai suna Sulaiman Jika, wanda ya rasu a ranar Juma’ar da ta gabata a makarantar horas da ‘yan sanda ta Najeriya (POLAC), da ke Wudil. Jihar Kano.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce mataimakin babban sufeton ‘yan sanda mai kula da sashen binciken manyan laifuka (FCID), Abuja, DIG Abiodun Alabi ne zai jagoranci kwamitin.
A cewar Adejobi, kwamitin na da hurumin gudanar da cikakken bincike ba tare da nuna son kai ba kan al’amuran da suka shafi mutuwar ba.
Shugaban ‘yan sandan ya sanya wa’adin kwanaki hudu ga kwamitin ya gabatar da cikakken rahoton binciken da ya yi da kuma shawarwarin da ya bayar.












































