Tinubu ya karbi kungiyar Tijjaniyya ta duniya a Aso Rock

Darikar Tijjaniyya, Kungiya, Tinubu, Aso rock
Da yake jawabi a lokacin da ya karbi tawagar kungiyar Tijjaniyya ta Duniya karkashin jagorancin Khalifa Muhammad Mahe Niass a fadar shugaban kasa da ke...

Da yake jawabi a lokacin da ya karbi tawagar kungiyar Tijjaniyya ta Duniya karkashin jagorancin Khalifa Muhammad Mahe Niass a fadar shugaban kasa da ke babban birnin tarayyar Abuja, a ranar Lahadin da ta gabata shugaban ya ce gwamnatinsa za ta goyi bayan tsare-tsare da kuma kokarin bayar da sauki da taimako ga alhazai.

Wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya sanya wa hannu ta ce, Tinubu ya jaddada muhimmancin ayyukan ibada wajen gina kasa yana mai jaddada kudirin gwamnatinsa na tallafawa ayyukan addini.

Ya yi nuni da bukatar yin hadin gwiwa tsakanin shugabannin siyasa da na kungiyoyi don ciyar da muradun kasa da inganta hadin kai a tsakanin al’umma.

Karanta wannan: Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi ‘ƴan kasuwar da ke ɓoye kayan abinci

A bangaren noma kuwa shugaban ya bayyana tsare-tsaren inganta noma ta hanyoyi daban-daban da suka hada da fadada filayen noma, samar da rance mai sauki ga manoma, da kuma zuba jari mai yawa a bangaren samar da noma.

“Mun sadaukar da kai wajen samar wa asibitoci kayan aiki na zamani da samar da kwararrun likitocin kiwon lafiya horo da kuma tabbatar da jin dadin jama’a ga kowane dan kasa, gami da cikakken inshorar lafiya.

Najeriya za ta zama mai fitar da abinci, za’a faɗaɗa samar da abinci sosai ta hanyar ingantattun injiniyoyi. Dole ne mu zama masu amfani a matsayinmu na mutane, wannan ita ce Sunna da ka’idojin da na taso na fahimta,” inji shi.

Karanta wannan: Kano: Kotu ta buƙaci a yiwa Hafsat Chuchu gwajin ƙwaƙwalwa

Tinubu ya godewa kungiyar Darikar Tijjaniyya ta Duniya bisa goyon baya da addu’o’in da suke yi, inda ya jaddada muhimmancin kokarin hadin gwiwa wajen gina Najeriya mai inganci.

Sheikh Mahe Niass Khalifan Tijjaniyya, wanda yake magana a madadin tawagar ya yabawa shugaba Tinubu bisa jajircewarsa na tabbatar da ci gaba da zaman lafiya a Najeriya.

Ya bayyana amincewa da shugabancin shugaban kasar tare da mika goyon baya da addu’o’in ‘yan kungiyar Tijjaniyya ta Duniya ga shugaban Najeriya.

A yayin ziyarar tasu tawagar ta gabatar da addu’o’in ci gaban kasa da hadin kai tare da yiwa shugaban kasa fatan nasara.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here