Kano: Hisbah ta kwace kwalaban giya tare da kama mata masu zaman kansu

hisbah, kama, kano, azumi, ramadan
Hukumar Hisbah ta kama mutane 11 a ranar Talata waɗanda aka ga suna cin abinci a lokacin azumin watan Ramadan a jihar Kano. Kano guda ce daga cikin mafi...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kwace kwalaben barasa akalla dubu 8,600 da aka loda cikin wata mota da ta shiga jihar daga Kaduna.

Jami’in hukumar da ke yaki da kayan maye, Idris Ibrahim wanda ya bayyana haka ga yan jarida a karshen mako, ya ce an kwace barasar ne ranar Alhamis da ta gabata a kauyen Kwanar Dangora da ke kan babbar hanyar Kano zuwa Kaduna.

Jami’in na bayyana cewa jami’an Hisbah sun yi ta bibiyar motar daga Kaduna har ta isa Kano.

Karanta wannan: Tinubu ya karbi kungiyar Tijjaniyyar duniya a Aso Rock

Ya ce “mun tsayar da motar a Kwanar Dangora inda direban ya yi yunkurin tserewa sai dai jami’anmu sun kama shi.”

Ibrahim ya kara da cewa tawagar hukumar da ke yaki da kayan maye suna dakon umarni daga manyan jami’an Hisbah.

A cewarsa, Hisbah ta kuma kama yan mata 15 masu zaman kansu a wurare daban-daban na jihar Kano.

Karanta wannan: Hukumar karbar korafi da yaƙi da rashawa ta Kano za ta binciki masu ɓoye kayan abinci

Bayanai na cewa an kama matan ne a unguwannin Hotoro da Tishama da Sabon Gari da titin Miyangu da titin Hadeja da kuma tsohuwar tashar mota da ke Titin Zoo Road.

Mataimakin babban kwamandan hukumar, Dakta Mujahid Aminuddeen wanda ya tabbatar da kamen ya ce an sha kama wasu daga cikin wadanda ake zargi masu zaman kansu ne inda aka gurfanar da su gaban kotu amma sun ci gaba da aikata haramtacciyar sana’ar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here