Sarauniyar wanzar da zaman lafiya ta farko a kasar nan Ambasada Hassana Saminu Turaki, ta ce babu wata al’umma da zata ci gaba matukar babu Zaman Lafiya.
Sarauniyar zaman lafiyar Amb. Dr. Hassana Saminu Turaki, ta bayyana hakan ne yayin da ake karramata da shaidar Digirin Digirgir na girmamawa har guda biyu, daga jami’ar Northewest International dake kasar Armenia da kuma kwalejin European Institutue of Apply research dake kasar Instonia.

A yayin taron dai wanda kungiyoyin Diflomasiyya na Duniya da na kare hakkin Dan Adam na Nahiyar Africa da kuma kasar nan suka shirya, Amb. Dr. Hassana Saminu Turaki, wadda ta kasance Yar gwagwarmayar kare hakkin Dan Adam musamman Mata da Yara Kanana, ta yi alkawarin ci gaba da ayyukan wanzar da Zaman Lafiya tare da tabbatar da’Yancin al’umma musamman Mata da Yara.
“Zamu ci gaba da taimakawa al’umma da yardar Allah, kuma zamu ci gaba da fafutukar kwato hakkin mata da Yara kanana tare da rajin tabbatar da Zaman Lafiya ya wanzu” inji Amb. Dr. Hassana.

Amb. Dr. Hassana Saminu Turaki ta kuma jaddada bukatar dake akwai cewa akwai rawar da hukumomi a kasar nan za su taka domin ganin zaman lafiya ya wanzu a tsakanin al’umma.
A yayin taron dai an karrama mashahuran mutane da lambar Digirin Digirgir 16, tare kuma da karrama wasu da shaidar Jakadun wanzar da zaman lafiya.














































