Satar jarrabawa: Yan sanda sun kama dalibai 10 sakamakon zane malamin su da sukai

0

Hukumar yan sandan jihar Ogun ranar Lahadi a Abeokuta ta ce ta kama dalibai 10 na makarantar sakandare sakamakon cen zarafin malamin su da sukai.

Kakakin rundunar ta yan sandan, Omolola Odutola ya ce sun kama daliban ne bayan malamin nasu mai suna Kolawole Shonuga ya shigar da karar daliban nasa a ofishin su.

Shonuga yace ya hana daya daga cikin daliban  satar jarrabawa a makaranta.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa (NAN) ya tattaro rahoton cewa abin ya faru ranar Talata a makarantar Ishanbi Comprehensive High School  Ilisan-Remo dake karamar hukumar Ikenne a jihar ta Ogun.

“Malamin ya je kwace takardar jarrabawa ta dalibin mai shekaru 18, bayan ya kamashi yana satar jarrabawa. Da aka tashi daga jarrabawa ne dalibin ya gayyato abokan sa wadanda suma dalibai ne suka tarewa malamin hanya, inda suka dinga dukan sa da sanda.” Inji Kakakin.

kakin yan sandan ya ce sunan suna gudanar da bincike, kuma rundunar bazata lamince irrin wannan abu ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here