Mata hudu da suka hada da daliba daya wadan da yan bindiga sukai garkuwa da su a jihar Zamfara, sun ce yan bindigar da sukai garkuwar da su sun yi musu barazanar auren su idon har iyayen su suka kasa biyan kudin fansa Naira miliyan 12.
Wadan da akai garkuwar dasu a hanyar Birnin Magaji-Kaura Namoda ya yin da suke dawo wa daga daurin aure, sun bayyana hakan ne a wani fefen video da aka saki ranar Asabar.
Matan da akai garkuwar da su sun hada da Ummukhair, Aisha Yahaya, Jemila Yahaya da kuma Ummu Sani, sun kara da cewa yan bindigar sun basu sati daya a kawo musu kudin ku su aure su.













































