Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya rufe shari’ar da ake yi da shi a kotun zabe bayan ya gabatar da sakataren gwamnatin jihar a matsayin shaida shi kadai.
Dr Abdullahi Baffa Bichi ya ce an ayyana wanda ake kara na biyu wato Abba a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Kano bayan ya samu kuri’u 1,019,602 wajen doke Dr Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC wanda ya samu kuri’u 890,705 da tazarar kuri’u 128,897.
Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kano ta yi zama a ranar Asabar, 22 ga watan Yuli don ci gaba da shari’ar da APC ta shiga a gabanta.












































