Tsohuwar Kwamishina A Kano Zubaida Damakka Ta Rasu

IMG 20230722 WA0182 639x430
IMG 20230722 WA0182 639x430

Rahotanni sun tabbatar da cewa Allah Ya yi wa Barista Zubaida Damakka Abubakar rasuwa a wannan Asabar din.

Za a yi jana’izar ta a gobe Lahadi da karfe 9 na safe a gidansu da ke Unguwar Gwammaja.

Marigayiyar tsohuwar kwamishina ce a Ma’aikatar Harkokin Mata da Ma’aikatar Kasafi da Tsare-Tsare ta Jihar Kano.

Haka kuma, har zuwa lokacin rasuwarta, ita ce Manajar Kamfanin Madara na L&Z.

Barista Zubaida na daya daga cikin kwamishinoni biyar da tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya sauke a watan Oktoban 2017.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here