‘Yan bindiga sun sace wani Basarake a jihar Pilato

Gunmen
Gunmen

A ranar Lahadin nan ne ‘Yan bindiga suka sace Charles Mato Daka, wani basaraken garin Gindiri dake karamar hukumar Mangu ta Jihar Filato.

Mai magana da yawun rundunar Operation Safe Haven ta sojojin Najeriya a Filato, Manjo Ishaku Takwa, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya shaida wa manema labarai a Jos cewa an yi garkuwa da Mato ne a gidansa dake Gindiri.

Ya ce an tura jami’an tsaro zuwa wurin da abin ya faru domin bin sawun maharan.

“Dakarun OPSH da ke Gyambus a Mangu sun tafi zuwa yankin. Suna kan hanyar bin sawun masu garkuwa da mutanen,” in ji Takwa.

NAN

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here