Garba Shehu ya kamu da cutar Covid-19

Garba Shehu1
Garba Shehu1

Babban mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da Mallam Garba Shehu ya kamu da cutar COVID-19 kuma yana killace a halin yanzu.

Sadai duk da haka Shehu, wanda ya tabbatar da hakan ga gidan talabijin na Channels a ranar Asabar, ya ce yana jin jikinsa da koshin lafiya.

Ya bayyana cewa yana jin alamun cutar kadan-kadan yanayin da ke da alaƙa samfurin omicron, inda ya kara da cewa ya killace kansa kuma zai je ya kara yin gwaje-gwaje don sanin matsayinsa.

Mai magana da yawun shugaban wanda aka yiwa cikakken rigakafin ya kuma tabbatar da cewa babban sakatare a fadar shugaban kasa, Tijjani Umar, da wasu ‘yan tsiraru a fadar Aso Rock suma an yi musu gwajin COVID-19.

Sai dai ya ce ba shi da masaniya kan sakamakon su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here