Gobara ta lalata shaguna 500 a kasuwar Terminus da ke Jos

Jos Terminus Market 720x430 (1)

Wata gobara da ta tashi da tsakar dare talalata sama da shaguna 500 a kasuwar Terminus da ke Jos a jihar Filato.

Misis Joyce Ramnap, kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar, ta tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a ranar Laraba a Jos.

Ramnap, wanda ya ziyarci wurin, ya ce lamarin ya faru ne da tsakar daren ranar Laraba.

Kwamishinan ya yi alkawarin cewa gwamnati za ta yi bincike domin gano musabbabin tashin gobarar.

Karanta: Majalisar harkokin Shari’ah ta naɗa Sheikh Umar a matsayin sabon shugabanta na kasa
“Daga rahoton shaidun gani da ido, musamman daga shugabannin kasuwar, mun tattaro cewa wutar lantarki ce ta haddasa tashin gobarar.

“Amma ba za mu bar shi a haka ba, za mu yi bincike don gano musabbabin tashinta”.

“Wannan abin takaici ne saboda an lalata fiye da shaguna 500; wannan babban asarar tattalin arziki ne ga jihar,”.

Ramnap, wanda ya jajanta wa ‘yan kasuwar, ya yi kira ga mazauna jihar da su daina yada labaran karya game da lamarin a shafukan sada zumunta.

Shugaban kasuwar, Mustapha Ibrahim, wanda ya koka kan irin dimbin asarar da ‘yan kasuwar suka yi, ya yi kira da gwamnati ta sa baki domin magance matsalolin ‘yan kasuwar da abin ya shafa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here