Shugaban hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh, ya bayyana ranar 9 ga watan Mayu a matsayin ranar da za a fara jigilar Maniyyata aikin hajjin bana zuwa kasa mai tsarki.
Saleh ya bayyana haka ne a wajen taron masu ruwa da tsaki na aikin Hajji na kasa a ranar Laraba, mai taken “Dorewar Tallafin Aikin Hajji: Samar da da tsari ga Alhazan Najeriya da Ma’aikata.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa hukumar NAHCON da hadin gwiwar bankin Jaiz ne suka shirya taron.
A cewar Saleh, NAHCON a matsayinta na mai kula da harkokin Hajji a Najeriya da kuma alhazan Najeriya da ke kasar Saudiyya, ta shirya tsaf domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2025 ba tare da wata matsala ba.
Ya bukaci masu ruwa da tsaki da su kasance masu hadin kai tare da jajircewa wajen samar da ingantattun ayyuka ga “bakin Allah masu daraja”, ta yadda za a karfafa sabon fata ga mahajjatan Najeriya.
Saleh ya godewa shugaban kasa Bola Tinubu da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima bisa goyon bayan da suke ci gaba da bayarwa da kuma sa baki a kan lokaci wajen magance kalubalen da ke fuskantar Hajjin 2025.
Shugaban Hukumar NAHCON ya ce taron ya samar da wani muhimmin dandali ga masu ruwa da tsaki daga bangaren gwamnati da masu zaman kansu domin yin nazari tare da tinkarar al’amura masu muhimmanci don dorewar ayyukan Hajji.
Ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa taron zai samar da tsare-tsare masu amfani na gudanar da ayyukan Hajji a Najeriya.
A nasa jawabin mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta nuna jajircewarta wajen ganin an samu nasara tare da inganta ayyukan Hajji a Najeriya cikin shekaru biyu da suka gabata.
Bashir Maidugu ne ya wakilci Shettima daga ofishin mataimakin shugaban kasa.
Mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta bayar da goyon baya sosai wajen gyare-gyaren hukumomi da nufin karfafa hukumar NAHCON da sauran masu ruwa da tsaki, ta yadda za a kafa harsashin samar da juriya da dogaro da kai.
A cewarsa, hauhawar farashin da ke tattare da aikin Hajji, tare da tabarbarewar tattalin arziki da kuma rashin tabbas a duniya, na nuna wajibcin samar da ingantaccen tsarin samar da kudade na aikin Hajji da Umrah. (NAN)













































