Fadar shugaban kasa ta bayyana labarin da ake yadawa na korar ministocin tsaro Muhammad Badaru Abubakar da Bello Matawalle da na wuta Adebayo Adelabu a matsayin labaran karya.
A wani sako da aka wallafa a shafin X na Bayo Onanuga a ranar Talata, ya bukaci hukumomin tsaro da su dauki matakin gaggawa kan kafafen yada labarai na karya da kuma masu satar bayanan karya wadanda suka kasa tantance sahihancin labarai.
Sanarwar ta ce, labarin mai taken “Da ɗumi-ɗumi: Tinubu ya kori ministocin tsaro da wutar lantarki”, wanda Phoenix Browser ya buga, gaba daya karya ne, yaudara, kuma ba shi da wani tushe na hakika.
Ko kadan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bai kori ministocin tsaro ko na wutar lantarki ba.
Idan ma rahoton kwanaki ne da aka samar da sauye-sauyen majalisar ministocin da aka sanar a watan Oktoba na 2024 ba su haɗa da ministocin tsaro ba.
Wadanda abin ya shafa sun hada da ministocin harkokin mata, yawon bude ido, ilimi, gidaje da raya birane, da ci gaban matasa. Bugu da kari, an sake nada ministoci goma, sannan an gabatar da sabbin sunayen mutane bakwai don tabbatar da su a majalisar dattawa, dukkansu an rubuta su a hukumance kuma kafafen yada labarai masu inganci sun ba da labarinsu.













































