Babban Bankin Najeriya (CBN) ya tabbatar da cewa bankunan ajiya na kasarnan (DMBs) suna nan daram duk da kalubalen tattalin arzikin cikin gida da na kasashen waje da ake fuskanta.
Gwamnan CBN, Yemi Cardoso, ya bayyana hakan a ranar Talata a Abuja yayin gabatar da sakamakon taron kwamitin manufofin kudi (MPC) karo na 298.
Cardoso ya ce kwamitin ya yaba da ci gaba da tsayuwar dakan tsarin banki duk da matsalolin tattalin arziki.
“Manyan alamun lafiyar kudi, irin su Capital Adequacy Ratio (CAR), Non-Performing Loan ratio (NPL), da Liquidity Ratio (LR), suna nuna karfin wannan fanni,” in ji shi, yana mai cewa CBN zai ci gaba da sa ido sosai don tabbatar da cewa bankuna na bin ka’idojin dokoki.
Kwamitin MPC ya kuma jaddada kokarin CBN na fadada shigar da mutane cikin tsarin hada-hadar kudi, domin inganta tasirin aiwatar da manufofin kudi.
Game da hauhawar farashi, Cardoso ya nuna cewa bayanai daga Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) sun nuna karuwar hauhawar farashi zuwa kashi 33.88% a watan Oktoba, daga kashi 32.70% a watan Satumba.
A kan kari-kari na wata zuwa wata, hauhawar farashin ta karu zuwa 2.64% a watan Oktoba daga 2.52% a watan da ya gabata.
Hauhawar farashin abinci ta tashi zuwa kashi 39.16% a watan Oktoba daga 37.77% a watan Satumba, yayin da hauhawar farashin kayayyakin yau da kullum (core inflation) ta tashi zuwa kashi 28.37%, idan aka kwatanta da 27.43% a watan da ya gabata.
Duk da wannan yanayin hauhawar farashi, kwamitin MPC ya lura da dan sassaucin farashin kayan gona kuma ya yaba wa kokarin Gwamnatin Tarayya na kara habaka samar da kayan amfanin gona.
Game da ci gaban tattalin arziki, Cardoso ya bayyana cewa Jimillar Kayayyakin Cikin Gida (GDP) na Najeriya ya karu da kashi 3.46% daga shekara zuwa shekara a zangon uku na shekarar 2024, wanda bangaren mai da wanda ba na mai ba suka taimaka.
Bangaren da ba na mai ba ya karu da kashi 3.37%, yayin da bangaren mai ya samu ci gaban kashi 5.17%.
Bugu da kari, ajiyar kudin waje ta Najeriya ta karu zuwa dala biliyan 40.88 a ranar 21 ga Nuwamba, daga dala biliyan 40.06 a karshen Oktoba, wanda zai iya daukar watanni 17 na shigo da kaya.