Harin Borno: Tinubu ya umarci hukumomin tsaro su ƙara tsaurara matakan tsaro – Shettima

Kashim Shettima 750x430

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya tana tura ƙarin rundunonin dabarun tsaro zuwa yankin da ‘yan ta’adda suka kai hari a birnin Maiduguri, domin bibiyar masu laifin tare da cafke su.

Shettima ya yi Allah-wadai da fashewar bam ɗin da ta yi sanadin mutuwar mutane biyar tare da jikkata wasu da dama a wani masallaci da ke kasuwar Gamboru a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, inda ya bayyana harin a matsayin mummunan ta’addanci kan fararen hula da zaman lafiyar ƙasa.

Ya bayyana cewa Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayar da umarnin gaggauta ƙara tsaurara ayyukan tsaro a fadin jihar Borno bayan wannan lamari, domin dakile duk wata barazana ga tsaro da kuma hana sake faruwar makamancin haka.

Mataimakin shugaban ƙasar ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya na aiki kafada da kafada da gwamnatin jihar Borno da hukumomin tsaro na cikin gida, domin tabbatar da kariya ga al’ummomi masu rauni da muhimman ababen more rayuwa a yankin Arewa maso Gabas da sauran sassan ƙasar.

Ya jaddada cewa gwamnatin tarayya ba za ta lamunci duk wani yunkuri da zai lalata zaman lafiya da tsaron ƙasa ba, inda ya tabbatar da cewa hukumomin tsaro suna aiki ba dare ba rana domin tabbatar da cewa an kamo masu aikata wannan mummunan laifi tare da hukunta su bisa doka.

Karin labari: Zulum ya yi Allah wadai da harin masallaci a Maiduguri, ya yi kira da a  ƙara yin taka tsantsan

Shettima ya nuna tausayinsa ga gwamnatin jihar Borno, mazauna yankin da iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a harin, yana mai bayyana cewa tsarin tsaron da ake da shi zai gano dukkanin bayanan da suka shafi harin.

Ya kuma jaddada cewa, tabbatar da adalci, tare da jaddada cewa jajircewar gwamnatin Tinubu wajen kare tsaro, haɗin kai da kwanciyar hankalin ƙasa na nan daram bisa kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here