Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, bayyana a jiya cewa wasu mutane sun yi kokarin haddasa sabani tsakaninsa da Shugaba Bola Tinubu watanni uku bayan rantsuwarsu, inda suka gargadi shugaban da ya daina sanya tufafin gargajiya da ya ba shi lokacin yakin neman zaben shekarar 2023.
Da yake jawabi a wujen gabatar da littafin tarihin rayuwar tsohon shugaban mulkin soji, Yakubu Gawun, a Abuja. Shettima ya ce wadanda ke bayan shirin na zargin cewa an yi sihiri a cikin tufafin don kashe shugaban kasar.
“Lokacin da muke yakin neman zabe a APC, muna zagaye a Arewa, sai na samu wasu kayan ado da huluna don ya saje da al-ummar Arewa, “sun masa kyau sosai.” Sai mataimakansa suka ce, “A sake yi masa wasu, sun yi masa kyau,” in ji Shettima.
“Watanni uku kacal bayan rantsuwarmu, wasu mutane na daga Borno sun zo wurinsa suka ce, ‘Ka daina sanya wadannan tufafin na Shettima. Dole ya yi musu sihiri. Kuma za ka mutu. Shi kuma zai zama shugaba.’
“Saboda adalcin shugaban kasa, lokacin da na dawo daga China, inda na wakilce shi, ya ce, ‘zauna. Mutanenka sun zo wurina suka ce na daina sanya tufafin da ka ba ni.’
“Amma ya ce labarinsu bai hadu ba saboda lokacin da ka ba ni wadannan tufafin, ni dan takara ne kawai.
“Tsawon mako guda, don ya nuna musu ba wani sihiri, ya sanya wadannan tufafin, wadannan su ne wasu daga cikin dabaru da ke faruwa a cikin harkokin mulki a Najeriya a yanzu.”
Ya ce babu al’amari na rashin amincewa lokacin da Gowon yake shugaban soji, inda ya kara da cewa iyalin Sarkin Sokoto na lokacin kan aika “galan-galan na fura” kowane mako zuwa Dodan Barracks da ke Legas, kuma shugaban kasar kan karbi kyautar ba tare da zargi ba.
“Rayuwarsa ta nuna cewa mutum zai iya daukar asali ba tare da kiyayya ba, tarihi ya koya mana cewa ci gaban Najeriya yana karfafa duk lokacin da ‘yan kasa suka ki bari su zama makaman da kungiyanci da rarrabuwa zai yi amfani da shi.”
Da yake ci gaba da magana kan manufofi da nasarorin tsohon shugaban soji, mataimakin shugaban kasar ya ce matsayin Gowon a tarihin ya wuce iya Najeriya.
“A matsayinsa na daya daga cikin wadanda suka hadi kan Afirka, kafa Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka ya kasance daya daga cikin manyan ayyukan da hangen nesa na siyasa a nahiyar,” in ji shi.












































