Kwankwaso aiki yake yi a boye don sake zaben Tinubu a 2027 – Bature

Sanusi Bature Dawakin Tofa 750x430

Mai magana da yawun Gwamnan Jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya zargi tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, da yin aiki a boye ga Shugaba Bola Tinubu gabanin babban zaben 2027.

Bature ya jaddada cewa hadakar siyasa da ake tsammani tsakanin Kwankwaso da Peter Obi na dan lokaci ne kawai kuma ba zai dawwama ba.

SolaceBase ta ruwaito cewa an amince wa Peter Obi ranar Laraba ya fafata a zaben fidda gwani na shugaban kasa a Jam’iyyar NDC, kuma Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana shirinsa na yin aiki da shi a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa.

A wata hira da ya yi a shirin Morning Show na Arise Television ranar Laraba, Sanusi Bature ya ce NNPP ba jam’iyyar siyasa mai karfi ba ce a zaben 2027, yana mai cewa tattaunawar cikin gida ta kai ga cimma matsaya kan wasu zabubuka da suka hada da jam’iyyar mai mulki ta APC.

Bature ya kara da cewa an yi tattaunawa tsakanin manyan ‘yan siyasa a Kano kan yiwuwar sake daidaitawa. “Da yardar Kwankwaso, muka kusanci Tinubu da APC a matsayin zabi na farko don binciko yiwuwar shiga jam’iyyar, don mu samu damar shiga FEC.”

Ya kara da cewa Kwankwaso da kansa da farko ya nuna sha’awar ganawa kai tsaye da Shugaba Tinubu domin tattaunawar siyasa, amma daga baya ya watsar da tsarin lokacin da shirin tafiya ya taso ba tsammani. “Kwankwaso ya dage kan yin magana da Shugaba Tinubu kafin duk wani sauya sheka, sai dai bayan an saita ranar, ya soke alkawarin, yana mai cewa zai je China, kuma bai sake tsara wani lokaci ba.”

Ya kuma ki yarda da hasashen da ke yawo kan yiwuwar hadin gwiwar siyasa tsakanin Kwankwaso da Peter Obi, yana mai cewa ba ta dace da yanayin siyasar Najeriya ta yanzu ba. “Tikitin Peter Obi-Kwankwaso a Kano abin ban mamaki ne, Kwankwaso, mai digiri na uku, ya zama mataimakin Obi, wanda ke da digiri na daya kacal, bai kamaci Kwankwaso da muka sani ba, Ban ga wannan hadin kai da zai yi aiki ba.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here