Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya maye gurbin takwaransa na jihar Ekiti Kayode Fayemi a matsayin shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya.
Cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na kungiyar Abdulrazak Bello-Barkindo ya fitar, ta ce Tambuwal ya karbi mukamin ne a taron majalisar tattalin arzikin kasa da aka yi a Aso Rock Villa, Abuja, bayan da Fayemi ya mika masa kundin mukamin.
Sanarwar ta ce Tambuwal zai ci gaba da rike mukamin har zuwa watan Mayun shekara mai zuwa lokacin da za a gudanar da zaben gwamnoni.
Kafin sabon mukamin amatsayin sabon shugaban kungiyar gwamnonin, Tambuwal ya taba zama mataimakin shugaban kungiyar a karkashin Fayemi a cikin shekaru hudu da suka gabata.
Ya kara da cewa, “Kafin hakan gwamnan Ekiti ya amince da sakamakon zaben da hukumar zabe ta fitar, ya kuma godewa takwarorinsa da sauran mambobin majalisar bisa goyon bayan da suka bayar.
Dayake maida jawabi mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ce shugaban kungiyar gwamnonin ya karbi ragamar shugabancin.
Sanarwar ta ce “Dr Fayemi ya mika ragamar shugabancin kungiyar gwamnonin ga Rt Hon Amuinu Waziri Tambuwal a ranar 16 ga Oktoba.”













































