Babban Sakatare na musamman kuma makusanci ga Atiku Abubakar kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Barr. Abdullahi Nyako ya rasu.
Cikin wata sanarwa da mai baiwa Atiku Abubakar shawara kan harkokin labarai Paul Ibe ya fitar, ta ce Barr. Nyako ya rasu da sanyin safiyar Alhamis.
Sanarwar ta ce, ‘’Ya kasance lauya kuma wanda ya dade yana hulda da tsohon mataimakin shugaban kasar.
“Abdullahi ya fi mataimaki, dan uwa ne gare ni ta kowace fuska.
Yayi aiki da ni cikin aminci da himma kuma za a yi kewarsa sosai. A madadin iyalaina ina mika sakon ta’aziyyata ga iyalan Nyako tare da addu’ar Allah Madaukakin Sarki, ina musu ta’aziyya ya kuma kara musu kwarin guiwa. Allah ya gafarta masa” inji Atiku.













































