Bankin Jaiz PLC ya nada Dakta Sirajo Salisu a matsayin Manajan Darakta kuma babban Jami’in Gudanarwa na bankin.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren bankin Muhammad Shehu ya fitar a birnin Legas.
Ta cikin sanarwar, Shehu ya ce nadin zai fara aiki ne daga ranar 16 ga watan Oktoba Mai kamawa.
Salisu,dai zai maye gurbin Manajan Darakta Mai barin gado, Malam Hassan Usman, wanda zai kammala aiki a wata Mai kamawa.
Kafin kaiwa ga nadin nasa, Salisu ya kasance Babban Darakta na Bunkasa Kasuwanci a shiyyar Arewa.
Ya fara aikin banki ne a shekarar 1992 tare da bankin Inland Plc a matsayin mai kula da harkokin banki, inda ya kai matsayin babban manaja a shekarar 2009 da bankin Inland Bank Plc.
A lokacin da yake hidimtawa bankin, ya rike mukamai da dama da suka hada da sashin kula da bashi da bunkasa kasuwanci, kafin ya zama Manaja na yankin babban birnin tarayya Abuja.
A 2009, an nada shi a matsayin Manajan Darakta a bankin musulunci na gambia mukamin da ya rike har zuwa watan Janairun Shekarar 2015.
Salisu ya shiga aikin bankin Jaiz ne a shekarar 2016 kuma ya rike mukamin Manaja na yankin kudu yayin da yake kula da sashen baitul malin bankin.
A shekarar 2018, an nada shi Babban Jami’in kulada tantance asara na bankin, inda daga baya ya kai matsayin Babban Darakta.













































