Dan tsohon mataimakin gwamnan Kano ya shigar da korafi ga ‘yan sanda, yana zargin Sunusi Bature da bata suna

Sanusi Bature Dawakin Tofa 1 750x430

Mujahid Aminu Abdussalam Gwarzo, dan tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Aminu Abdussalam Gwarzo, ya gabatar da korafi ga Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano kan zargin da yake yi wa Sunusi Bature Dawakin Tofa, mai magana da yawun Gwamna Abba Kabir Yusuf, na yin maganganu na bata suna akan shi.

SolaceBase ta ruwaito cewa an gabatar da korafin mai kwanan wata 17 ga Yuni 2026, ta hannun kamfanin lauyoyi A.A. Shirawa, Nasirudeen & Partners, kuma Barrister Nazifi Yusuf Gorondutse ya sanya hannu.

A cewar korafin, Sunusi Bature, wanda ke aiki a matsayin Darakta Janar na Sadarwa da Yada Labarai ga Gwamna Abba Kabir Yusuf, an zarge shi da yin kalamai a wani taron siyasa a Kano ranar 13 ga Yuni, inda ya zargi Mujahid Gwarzo da karbar kudin fansho, wanda aka fi sani da “Awwalaja,” daga shugabannin kananan hukumomi 44 na jihar.

Korafin ya ƙara zargin cewa Sunusi Bature ya ce an ba da kuɗin ga mahaifin Mujahid, tsohon Mataimakin Gwamna kuma tsohon Kwamishinan Kananan Hukumomi, kuma an yi amfani da su wajen siyan filaye da gonaki.

Lauyoyin mai karafi sun koka cewa an yada zarge-zargen ta hanyar bidiyo da ya yadu a shafukan sada zumunta, lamarin da ya haifar da babbar illa ga mutuncin wanda suke karewa.

Saboda haka gungun lauyoyin ta bukaci ‘yan sanda da su binciki lamarin da ɗaukar mataki kan abin da suka kira bata suna da kassara mutunci.

Wannan sabon lamarin shi ne ba baya-baya da ake musayar kalamai na siyasa da ke ƙaruwa tsakanin manyan ‘yan siyasa a Jihar Kano yayin da harkokin siyasa gabanin zaɓen 2027 ke ci gaba da ƙaruwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here