Shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Umar Ganduje ya nemi gwamnan Jihar Kano Abba Kabri Yusuf na jam’iyyar NNPP ya koma jam’iyyar su ta APC.
Ganduje ya mika goron gayyatar ne ga Gwamna Abba Kabir a wani taron jiga-jigan APC da ya gudana a Kano.
Karanta wannan: Ganduje ya Jagoranci shugabannin APC na Kano zuwa ganawa da Tinubu a Villa
Tsohon gwamnan na Kano ya ce muddun Abba Kabir ya koma APC to kuwa zai mayar da Kano mai bin tafarki jam’iyya guda.
Ganduje ya kara da cewa Apc ta kudiri aniyar hadiye dukkan kananan jamiyyun dake kasar nan.
Dr. Ganduje ya ce APC a shirye ta ke ta karbi Abba Kabir Yusuf da magoya bayansa hannu bibbiyu ba tare da wata-wata ba.













































