Masu Hakar Ma’adanai Ba Bisa  Ka’ida Ba Sun Mutu A Jihar Nasarawa

Nasarawa Map

Wasu masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba su uku sun muta sakamakon ruguzowarvkasa a kansu, lokacin da suke tono tare da lodin yashi a kauyen Unguwar Tandu da ke karamar hukumar Karu a jihar Nasarawa.

Mataimakin shugaban kungiyar masu aikin dibar yashi, Aminu Sunusi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya bayyana cewa mutane uku ne suka rasa rayukansu yayin da mutum daya da ya tsira da ransa ke karbar kulawar gaggawa a asibiti.

Ya ci gaba da cewa, “Marigayin suna hako yashi ne domin lodin wata babbar mota kirar ‘Tipper’ a wurin da ke Unguwar Tandu mai tazarar kilomita kadan zuwa Keffi amma tana cikin karamar hukumar Karu sai yashi ya zame ya rufe su.”

A cewarsa, an binne gawarwakin da aka gano kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Mohammed Nasir wanda ya tsira da ransa da Aruwa Maikasuwa, daya daga cikin iyayen mamatan sun ce har yanzu ba su farfaɗo ba daga bala’in da ya faru a unguwarsu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here