Hukumar zabe mai zaman kanta INEC reshen jihar Oyo ta tabbatar da tashin gobara a ofishin hukumar na karamar hukumar Ibadan ta kudu maso gabas.
A wata sanarwa da kwamishinan zaben jihar Dakta Adeniran Tella, ya fitar da yammacin Juma’a yace gobarar ta tashi ne da misalin karfe 10 da mintuna 30 na safe.
Karanta wannan: Yanzu-yanzu:Ganduje ya nemi Abba Gida-gida ya koma APC
Sanarwar tace har kawo lokacin rubuta wannan labari ba a gano musabbabinta ba.
A ranar Asabar 3 ga watan Fabrairu mai kamawa ne hukumar ta INEC zata gudanar da zabukan cike gurbi tare da sake wasu a jihohin kasar nan 9.