Gwamnatin Kano ta gargadi shugabannin kananan hukumomi kan siyar da kadarorin gwamnati ba bisa Ka’ida ba

Abba Kabir Yusuf Kano Governor 750x430

Gwamnatin jihar Kano ta gargadi shugabannin kananan hukumomi 44 da su dakatar da sayar da kadarorin gwamnati ba tare da izini ba a fadin jihar.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa gargadin na zuwa ne bayan samun wasu rahotanni da ke cewa ana zargin shugabannin kananan hukumomin da siyar da kadarorin gwamnati ba bisa ka’ida ba, wadanda suka hada da gonaki da filaye da shaguna.

Karanta wannan: Gwamnatin Kano za ta kashewa makarantun firamare 3 Naira Biliyan 8

Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, ya nuna matukar damuwarsa kan wadannan rahotanni tare da jaddada bukatar kare kadarorin al’umma.

Mataimakin gwamnan jihar kuma kwamishinan kananan hukumomi, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya yi gargadin cewa gwamnati za ta dauki kwararan matakai kan duk wanda aka samu da laifin sayar da kadarorin gwamnati.

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar kananan hukumomi Dahiru Lawan Kofar Wambai ya fitar a ranar Juma’a, ya ce Kwamared Gwarzo yace an aike da wata tawaga zuwa kananan hukumomi daban-daban domin ganowa tare da kama mutanen da ke da hannu a cinikin kadarorin gwamnati ba tare da izini ba.

Karanta wannan: 

Ta bukaci jama’a da su marawa kokarin gwamnati baya ta hanyar kwarmata mutanen da ke sayar da kadarorin gwamnati a fadin jihar.

A cewar sanarwar, hadin kan al’umma na da matukar muhimmanci wajen tabbatar da kiyaye kadarorin jama’a da kuma tabbatar da doka da oda.

Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar Kano za ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da gaskiya da rikon amana da kuma kare dukiyoyin al’umma, tare da tabbatar da cewa duk mutumin da aka samu da laifin aikata wannan ta’asa to zai fuskanci hukunci mai tsanani.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here