Gwamnatin Kano ta ware Naira biliyan 8 don gina manyan makarantun firamare uku a fadin jihar.
Manyan makarantun firamare, a cewar Gwamna Abba kabir Yusuf, za su kasance da cikakkun wuraren karatu, wanda hakan zai ba da isasshen yanayi ga yaran da iyayensu ba su da karfi don samun ingantaccen ilimi a nan gaba.
Karanta wannan: Hukuncin kotun koli: Sarkin Kano ya taya gwamna Abba Murna
Gwamnan ya ce za’a samar da manyan makarantun ne a kowace mazabar majalisar dattawa da kayayyakin koyo na zamani don samar da ingantaccen ilimi a matakin farko.
Ya kuma ce an ware naira biliyan 6 domin gyara dukkan makarantun firamare.
Hakazalika, ya ce gwamnati ta amince da gyara wasu cibiyoyi na musamman guda 26 da tsohon Gwamna Rabi’u Kwankwaso ya kirkiro wanda aka kammala 17 daga cikin su.
Karanta wannan: Yanzu-yanzu: An samu fashewar wani abu a Ibadan
“Za mu ci gaba da bada kulawa ga samar da kayan aikin koyarwa na yau da kullun da za su ba wa yaranmu damar samun ingantaccen yanayin koyo da koyarwa.
“Mun kuma kashe Naira miliyan 500 wajen gina hostel a Jami’ar Wudil sannan kuma an biya Naira miliyan 150 don sabon sashin kula da muhalli da yanayi na Jami’ar Maitama Sule.
“An biya Naira Miliyan 500 na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jiha don sabbin kwasa-kwasai a Wudil da Jami’ar Yusuf Maitama Sule.
Karanta wannan: Ministan bai ki amsa gayyatar mu ba- hukumar CCB
“Masu karatun shari’a na Kano da sauran cibiyoyi sun ci gajiyar biyan sama da Naira miliyan 100 domin yin rijistar sabbin kwasa-kwasansu.
“Kusan kashi 93 cikin 100 na Kudaden Karatu na Dalibai 501 na Masters a Indiya da sauran kasashen waje an daidaita su kuma an daidaita alawus din su na tsawon watanni hudu don ba su damar fuskantar karatunsu,” in ji shi.
Abba ya kuma ce gwamnati ta biya Naira miliyan 700 a matsayin kudin rijista ga daliban jihar Kano da ke karatu a jami’ar Bayero ta Kano, sannan ta biya Naira biliyan 1.5 a matsayin kudin jarrabawar WAEC da NECO ga daliban makarantun sakandire na jihar kamar yadda NAN ta rawaito.