Hukumar kare Muhalli ta Abuja (AEPB) ta dauki ‘yan kwangila 40 domin tsaftace birnin tarayya.
Daraktan hukumar Mista Osilama Braimah ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Abuja ranar Laraba.
Braimah ya ce hukumar za ta bi tsari wajen biyan ‘yan kwangilar, inda ya ce “mun biya su kashi 100 kuma babu wani dan kwangila da yake bin bashi”.
Ya bayyana cewa hukumar ta dauki nauyin kula da sharar gida da tsaftar gari a yankunan Maitama, Asokoro, Garki, Guzape, Katampe, Wuse, Mabushi, Wuye da sauran gundumomin da ke cikin birnin.
Sauran wuraren, in ji shi, sun hada da titin filin jirgin sama, har zuwa Bill Clinton, kusa da filin jirgin sama, da yankin kasuwanci na tsakiya da kuma titin Goodluck Jonathan, har zuwa axis na Karu.
Karin karatu: Likitoci a Abuja sun janye yajin aikin gargadi biyo bayan matakin Minista Wike
“Har ila yau, muna kawar da mabarata a birnin da kuma kula da gadojin masu tafiya a kafa don hana mutane amfani da su a matsayin kasuwa.
“Har ila yau, muna da alhakin kula da najasa a cikin birni da kuma wuraren biyan bukata a Wupa, Guzape, Katampe, da Apo, da sauran su”.
“A takaice dai, AEPB ce ke da alhakin aiwatar da duk wasu dokokin muhalli da kuma rage duk wani nau’i na lalata muhalli”.
Braimah ya ce an ba kowanne daga cikin ‘yan kwangilar 40 wani yanki na musamman domin kwashe sharar da kuma tsaftace wurin.













































