Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu satar mutane ne sun yi garkuwa da tsohon Darakta-Janar na jukumar kula da masu yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC), Manjo Janar Mahrazu Tsiga (mai ritaya).
An yi garkuwa da Tsiga, tare da wasu mazauna kauyen Tsiga da ke karamar hukumar Kankara a jihar Katsina.
Wani mazaunin yankin ya tabbatarwa da gidan Talabijin na Channels faruwar lamarin ta wayar tarho a ranar Alhamis.
Karin labari: Yan bindiga sun sace budurwa a Kano bayan karɓar miliyan takwas daga danginta
Ya ce, an yi garkuwa da mutanen ne a ranar Laraba bayan da wasu ‘yan bindiga dauke da manyan makamai suka mamaye gidan tsohon Darakta Janar na NYSC.
Har yanzu dai gwamnatin jihar Katsina da hukumar ‘yan sanda ba su fitar da wata sanarwa ba game da sace mutanen ba.
Shaidun gani da ido sun ce tsohon shugaban NYSC na cikin wadanda maharan suka yi garkuwa da su.
Majiyoyi sun ce a yayin harin da ya dauki ‘yan mintuna kadan, wasu mazauna garin biyu sun samu raunuka, daya daga cikin ‘yan bindigar kuma ya mutu bayan da abokan aikinsa suka harbe shi cikin kuskure.













































