Likitoci a Abuja sun janye yajin aikin gargadi biyo bayan matakin Minista Wike

doctors 1

 

Kungiyar Likitocin FCT ta janye yajin aikin gargadi bayan sa hannun Ministan FCT, Nyesom Wike, wanda ya biya bukatun su.

Shugaban kungiyar, Dr. George Ebong, ya ce an fara biyan likitoci albashin watanni shida da ake binsu.

Haka kuma, Minista Wike ya amince da biyan kudin kayan aiki, rage shekarun aiki na likitocin zama daga shekaru biyu, da daukar sabbin ma’aikatan lafiya don magance karancin ma’aikata.

Kungiyar ta umurci mambobinta su koma aiki daga ranar Asabar, 25 ga Janairu, 2025.

Duk da haka, Dr. Ebong ya bukaci Ministan ya ci gaba da magance sauran matsalolin da suka hada da biyan kudin gyaran asibitoci, da sauran bukatu don kaucewa yajin aiki nan gaba.

Ya jinjinawa kokarin Minista Wike kan sauya bangaren lafiya a FCT.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here