Likitoci sun dakatar da yajin aikin gargaɗi da suka fara

doctors

Kungiyar Likitoci masu neman kwarewa ta Najeriya (NARD) ta dakatar da yajin aikin gargadi da ta fara a ranar Juma’a, inda ta sanar da cewa za a koma bakin aiki daga ranar Lahadi.

Shugaban kungiyar, Dakta Tope Osundara, ya bayyana cewa gwamnati ta biya wasu daga cikin bukatun likitocin, sannan ta yi alkawarin duba sauran matsalolin da suke bukatar kulawa.

Ya ce dakatar da yajin aikin alamar kyakkyawar niyya ce domin taimaka wa marasa lafiya da ke bukatar kulawa a asibitoci.

Sai dai bai fayyace bukatun da aka cika ba.

Labari mai alaƙa: Likitoci sun fara yajin aikin gargaɗi na kwana biyar

Duk da haka, yajin aikin ya riga ya kawo cikas a hidimar asibitocin gwamnati, inda sauran likitoci da ma’aikatan jinya suka ɗauki nauyin marasa lafiya masu yawa, abin da ya jawo jinkiri wajen kula da su.

Likitocin sun fara yajin aikin ne don neman a biya musu kudin horo na Medical Residency Training Fund na shekarar 2025, bashin watanni biyar na karin albashi (25–35%), da kuma sauran bashin albashi da ake bin su.

Haka kuma sun nemi a biya musu bashin kayan aiki na shekarar 2024, a rika biyan kuɗaɗen ƙwararru akan lokaci, da kuma dawo da amincewa da takardar shaidar ƙwararru ta West African Postgraduate.

Bugu da ƙari, sun bukaci Kwalejin Likitocin Kwararru ta Najeriya ta rika bayar da takardar shaidar membobinsu, ta aiwatar da sabon tsarin albashi na 2024, tare da magance matsalolin walwalar likitoci a jihar Kaduna da kuma asibitin koyarwa na LAUTECH da ke Ogbomoso.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here